Connect with us

Labarai

Tsaftar Muhalli: Naburaska ya faɗa komar gwamnatin Kano

Published

on

Kwamitin tsaftar muhalli na ƙarshen wata-wata da gwamnatin Kano ta kafa ya cafke ɗan wasan kwaikwayon nan Mustapha Musty wanda aka fi sani da Naburaska.

An cafke ɗan wasan ne a unguwar Tudunwada dake ƙaramar hukumar Nasarawa bisa karya dokar zama a gida domin tsaftace muhalli har zuwa ƙarfe 10 na safe.

Mustapha Naburaska ya shaida wa Freedom Radio cewa ya fito ne domin zuwa jana’iza cikin rashin sani, amma yanzu ya fahimci cewa tsaftar muhalli ta kore kowanne uzri.

A ƙarshe kotun tafi da gidanka ƙarƙashin mai shari’a Auwal Yusuf Sulaiman ta ci tarar sa naira dubu biyar, amma daga bisani ya nemi afuwa tare da nuna nadamar sa, a don haka kotu ta yi masa sassauci ya biya naira dubu uku.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,958 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!