Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Tsananin matsi ya tilastawa al’ummar Kano komawa amfani da shinkafa Sanfurin a fafata

Published

on

 

Ya yinda ake fama da Tsadar kayayyakin masarufi a Nijeriya, Masu siyar da kayan abinci a Jihar Kano sun bayyana cewar yanzu magidanta musamman masu karamin karfi Basa iya siyan kayan abinci, musamman ma shinkafa, da akafi cinta a kowanne gida, Kuma akafi son amfani da ita fiye da sauran kayan abinci.

Hakan tasa yanzu magidanta suka koma siyan siyan wata shinkafa Mai datti da ake Kira da Afafata ko kuma ci karka mutu, sakamakon tsadar Shinkafar Mai kyau.

A zantawar freedom Radio da wata mata da taje siyan shunkafar Rabin kwanu a kasuwa ta bayyana cewar yanzu haka shinkafar samfurin afafata da kuma ci karka mutu su ne mafi muni da lalacewa kuma mafi saukin farashi wadda ake samun kwanu ta a farashin naira 1800 a yanzu, duk kuwa da cewa sai anyi mata hidima mai tarin yawa kafin amfani da ita.

 

Malam Abubakar Kabir wani Mai sana’ar awo ne a nan Kano, wanda yace “a yanzu koda masu dama-dama basa siyan buhun shinkafar balle masu karamin karfi, sai dai ayi awo, yayin da kaso mafi yawa suka fi mai da hankalin wajen siyan shinkafar da aka sawa suna ci karka mutu ko a fafata”.

 

Malam Abubakar Kabir dai ya ce” a halin da ake ciki a yanzu su kansu masu siyar da kayan awon sunfi cinikin shinkafar sanfurin afafata, fiye da shinkafa ta gida data waje”.

Al’umma dai na ta Kira ga Gwamnati da masu hannu da shuni dasu tausawa, tare da agazawa masu karamin karfin da a yanzu zaka iske gidaje da dama da suke yini, su Kuma kwana da yunwa, don haka masana suke ganin ya kamata a zage damtse wajen tallafawa masu karamin karfi da kuma lalubo hanyoyin saukakawa Al’umma matsin rayuwar da ake ciki daga gwamnatocin a dukkanin Matakai.

 

Rahoton:Abba Isa Muhammad

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!