Connect with us

Labarai

Tsananin zafi ne ya haddasa gobara a Giwa Barracks dake Maiduguri- Operation Hadin Kai

Published

on

Rundunar sojojin Nijeriya ta tabbatar da tashin gobara a rumbun makamai da ke barikin sojoji na Giwa Barracks da ke birnin Maiduguri a Jihar Borno ta arewa maso gabashin ƙasar.

 

Wata sanarwa da Reuben Kovangiya, muƙaddashin mataimakin mai magana da yawun rundunar Operation Hadin Kai, ya fitar ranar Laraba da maraice ta ce lamarin ya faru ne “a ɗaya daga cikin wuraren ajiyar makamanmu da ke Giwa Barracks.”

 

Ta ƙara da cewa “gobarar ta tashi ne sakamakon tsananin zafi da ake fama da shi a Maiduguri.”

 

Sai dai sanarwar ta ce an shawo kan gobarar sakamakon “ƙoƙari na haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Borno da kuma wasu motocin kashe gobara daga sauran hukumomin tsaro.”

 

Reuben Kovangiya ya shaida wa jama’a su yi watsi da rahotannin da ke cewa an kai sabbin hare-hare a birnin na Maiduguri da kewayensa.

 

Ya ce an tura dakarun rundunar Operation Hadin Kai lungu da saƙo na birnin domin hana ɓata-gari yin amfani da wannan dama wurin yin sace-sace da sauran ayyuka marasa kyau.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!