Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsarin zaɓen shugabannin jam’iyyar APC ya saɓa da doron Dimukuraɗiyya

Published

on

Masanin siyasa kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa ya ce, zaɓen shugabannin jam’iyyar APC da aka yi a baya-bayan nan ya saɓa da doron dimukuraɗiyya.

A cewarsa jam’iyyun siyasar Najeriya sun ɗauki wani tsari na lalata harkar demokradiyya gaba ɗaya.

Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa ya bayyana hakan jim kaɗan bayana kammala shirin Barka da Hantsi na tashar Freedom Radiyo wanda yayi duba kan zaɓen shugabanin jam’iyar APC da aka gudanar.

Daukawa ya ce “Tsarin da ƴan siyasa ke bi a yanzu ya gurgunta harkokin dimukuradiyya, musamman ma yadda a yanzu tun kafin a yi zaɓe ake iya bayyana sunan wanda zai ci zaɓen”.

“Haka kuma siyasar uban gida ta taka rawa wajen ƙara kawo naƙasu a harkar dimukuraɗiyya.

“Muna gani a yanzu yawanci wanda yake yin mulki shi ke ɗorewa akan kujerar sa, kuma shi yake da ikon ɗorawa da sauke duk wanda ya so ba wai abi cancanta ba”.

Dr Daukawa ya ƙara da cewa, “Magudin zaɓe ma na taka rawa wajen taɓarɓarewar tsarin dimukradiyya, idan aka yi duba da tsarin da aka bi wajen gudanar da zaɓen jami’yar ta APC ya saɓa da dimukradiyyar”.

Masanin ya yi fatan cewa samar da gyara a siyaysar ƙasar nan kafin zaɓen shekarar 2023 zai taimaka wajen samar da ingantaccen zaɓe da shugabanni na gari da kuma bunƙasa harkokin dimukraɗiyya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!