Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaro – Ƴan bindiga sun sace kwamishina a Neja

Published

on

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Neja Muhammad Idris.

Ƴan bindigar sun je gidan kwamishinan ne a ƙauyen Baban Tunga da ke ƙaramar hukumar Tarfa a ranar Lahadi tare da yin awon gaba da shi.

A zantawar shugaban karamar hukumar Ibrahim Mami da wakilinmu Nuradden Isyaku Daza ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ibrahim Mami ya ce, ƴan bindigar sun sace kwamishinan da misalin ƙarfe sha ɗaya na daren yayin da ake tsaka da ruwan sama a yankin, sai dai har zuwa yanzu basu nemi iyalan sa ba don fara tattaunawa ba.

Sai dai itama rundunar ƴan sandan jihar ta bakin mai magana da yawun ta Wasi’u Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin, amma dai bai yi ƙarin bayani akai ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!