Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

 NARD – A shirye muke mu janye yajin aiki

Published

on

Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa reshen asibitin Aminu Kano ta ce, a shirye ta ke ta janye yajin aikin da ta tsunduma.

Sakaren kungiyar Dakta Tahir Sani ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala shirin “Barka da Hantsi” na tashar Freedom Radio.

Dakta Tahir Sani ya ce, “Matukar gwamnati ta cika mana alƙawuran da muka kulla da ita, to kuwa za mu dawo bakin aiki ba tare da wani jinkiri ba”.

Sakataren kungiyar ya zargi cewa, gwamnatin tarayya ta gaza biyan su kuɗaɗen alawus-alawus na hatsarin aikin corona, da kuma albashin wasu daga cikin ma’aikata.

“Wannan ne ya sanya muka ga ba mu da wata mafita face mu tsunduma yajin aiki don jawo hankalin gwamnati” in ji Dakta Tahir Sani.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!