Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaro: An sake sace mutane 60 a Zamfara

Published

on

Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da sace mutane 60 a ƙauyen Rini dake ƙaramar hukumar Bakura ta jihar Zamfara a daren Jumma’a.

Mai magana da yawun rundunar SP Shehu Muhammad ne ya tabbatar da faruwar lamarin yayin zantawar sa da manema labarai.

Shehu ya ce, ‘yan bindigar sun sace mutane 60 ne ba 70 ba kamar yadda ake faɗa.

Sai dai wani shaidar gani da ido ya ce, masu garkuwa da mutanen sun shiga ƙauyen da ƙarfe biyu da rabi na dare, tare da yin harbe harbe, abinda ya haifar da guje-gujen jama’a don tsira da rai.

Akwai ‘yan bindiga sama da dubu talatin a jihar Zamfara – Majalisar Sarakuna

Kazalika maharan sun kai hari a ƙauyen Sabon Gari, da Makarantar Boko sai kuma kauyen Rini tare da sace sama mutane 70.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!