Connect with us

Labarai

Tsaro: Ba za mu yi sulhu da ƴan bindiga ba – Buhari

Published

on

Gwamantin tarayya ta ce ba za ta tattauna ko zaman sulhu da ‘yan bindiga da masu garakuwa da mutane ba.

Karamin Ministan Ilimi Chukwuemeka Nwajiuba ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

Nwajiuba ya ce, gwamnatin ta dauki matakin kin yin sulhu da masu tada hankalin jama’a ne, duba da cewa biyan su kudaden fansa na taimaka musu wajen mallakar makamai.

Ministan ya ce, gwamnatin tarayya na daukar matakan samarwa da dukkanin al’ummar kasar nan tsaro, ta hanyar yaki da ‘yan bindiga musamman ma a yankin Arewa maso gabas.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!