Labarai
Tsaro: Bayan shekara biyu an cafke wanda suka yi garkuwa da bature a Kano
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta cafke waɗanda ake zargi da kashe ɗan sanda tare da sace wani bature.
A ranar 16 ga watan Afrilu na shekarar 2018 ne wasu ‘yan bindiga suka buɗe wuta a titin Madobi inda suka harbe wani ɗan sanda Rabilu Musa.
Ƴan bindigar sun kuma ta fi da bindigar ɗan sandan tare da harsashi guda goma sha biyar.
Sannan suka yi awon gaba da wani Injiniya ɗan ƙasar Jamus mai suna Michel Cremza.
A ranar Talata jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanar da Freedom Radio kama waɗanda ake zargin bayan shafe shekara biyu.
Kiyawa ya ce, sun fara cafke wani matashi mai suna Abubakar Isma’il mai shekara 30 a duniya ɗan ƙauyen Wangara a ƙaramar hukumar Rimin Gado da ke Kano.
Binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin na da ruwa da tsaki wajen aikata ayyukan ta’addanci a Kano da Katsina da kuma jihar Kaduna a cewar Kiyawa.
You must be logged in to post a comment Login