Labarai
Tsaro: Dokar katse layukan waya na nan daram a Zamfara – Gwamna Matawalle
Gwamnatin jihar Zamfara ta ce, za a ci gaba da zama cikin dokar katse layukan waya.
Gwamnan jihar Muhammad Bello Matawalle ne ya bayyana hakan a zantawar sa da BBC Hausa.
Ya ce, za a ci gaba da zama ƙarƙashin dokar har sai lokacin da jami’an tsaro suka bada rahoto mai kyau ga me da yaƙi da ayyukan tsaro.
Ƴan bindiga sun ƙone gidan shugaban majalisar dokokin jihar Zamfara
Matawalle ya kuma ce, a yanzu ana ganin amfanin datse layukan wayar musamman yadda ƴan bindaga suke bayyana kan su sakamakon matsin da suka shiga.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, yanzu haka al’umma jihar Zamfara na fita zuwa jiha Sokoto da Funtua a jihar Katsina don yin kiran waya ko aika gajeren saƙo da sauran buƙatun su a wayar.
You must be logged in to post a comment Login