Labarai
Tsaro: harin yan ta’adda ya sanya mazauna Damasak tserewa zuwa Nijar
Ya zuwa yanzu, akalla mutane dubu dari ne suka tsere daga garin Damasak na jihar Borno zuwa Jamhuriyar Nijar mai makwabtaka da su a Larabar nan, sakamakon yawaitar hare-haren mayakan Boko Haram.
Hukumomin gwamnati sun ce aƙalla mutane 10 aka kashe a Larabar nan, yayin da wasu da dama suka ji rauni, kana wasu dubbai suka bazama cikin dazuka.
A cewar su, ya zuwa yanzu, akalla mutane dubu dari ne suka tsere daga garin Damasak na jihar Borno zuwa Jamhuriyar Nijar mai makwabtaka da su a Larabar sakamakon yawaitar hare-haren mayakan Boko Haram.
An kuma gano cewa daruruwan gidaje na farar hula, da shagunansu da gine-ginen gwamnati gami da hedkwatar rundunar ‘yan sanda sun kone kurmus sakamakon cinna musu wuta da maharan suka yi.
Harin na Laraba a Damasak, an sanya shi a jerin hare-hare mafi muni, wanda kuma shi ne na karo na shida a cikin makonni biyu da suka gabata.
Sai dai har kawo yanzu babu wata sanarwa a hukumance da ta fito kan matsayin garin, wanda ya zuwa yanzu kimanin shekaru 11 kenan yankin na fama da hare-haren ‘yan ta’addan.
You must be logged in to post a comment Login