Connect with us

Labarai

Tsaro: Kowa ya nemi matakin kare kan sa daga harin ƴan bindiga – Masari

Published

on

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya buƙaci al’ummar da suke zaune a yankunan da aka fi fuskantar matsalar tsaro da su ɗauki matakin kare kan su.

Masari ya bayyana hakan lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan waɗanda da suka rasa rayyukan su a Jibia.

Gwamna Aminu Masari ya gargaɗi mazauna jihar da su riƙa sanya idanu akan mutanen da suke mu’amala da su, tare da kai rahotan duk wanda suka ga basu amince dashi ba, don ganin an karkarɗe ayyukan ɓata gari a fadin jihar.

Har ma ya ce, al’umma za su iya kai bayanan sirri ga jami’an tsaro mafi kusa da su domin ganin an gudu tare an tsira tare.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!