Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaro: Tinubu ya nemi Buhari ya dauki matasa miliyan 50 aikin soji

Published

on

Jagoran jam’iyyar APC na kasa, kuma tsohon gwamnan jihar Lagos, Sanata Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki matasan kasar nan miliyan hamsin aikin soja.

Tinubu wanda ya bayyana haka a ranar litinin a Kano, ya ce hakan zai taimaka wajen inganta yakin da ake yi da ta’addanci da masu satar mutane don neman fansa da sauran ayyukan ‘yan bindiga da kasar nan ke fama da su.

Tinubu wanda ya zo Kano don gudanar da laccar cikarsa shekaru 69, ya bayyana cewa jami’n tsaron kasar nan sun yi karanci matuka, saboda haka akwai bukatar a kara yawansus.

‘‘Yanzu Najeria na rububin daukar matasa marasa aikin yi ayyukan tsaro hakan zai rage ‘yan fashi da makami da masu satar mutane don neman fansa’’.

‘‘Daukar matasa miliyan 50 aikin soja a Najeriya abu ne da zai yiwu don kuwa abincin da za su rika ci kamar masara da rogo da doya duk a cikin kasar nan za a rinka samar da su’’ a cewar Bola Ahmed Tinubu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!