Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari: Kasancewar Najeriya dunkulalliya ita ce kawai mafita

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai fi kyautatuwa Najeriya ta ci gaba da kasancewa a matsayin dunkulalliya domin hakan ne kawai zai kawo ci gaban kasa.

Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne yayin bikin cika shekaru sittin da tara da haihuwar jagoran jam’iyyar APC na kasa Sanata Bola Ahmed Tinubu wanda ya gudana a Kano a ranar litinin.

Shugaba Buhari ya ce yana cikin ‘yan mazan jiya da su ka yi yakin basasar Najeriya tsakanin shekarun alif da dari tara da sittin da bakwai zuwa shekarar dubu biyu da saba’in, saboda haka, ba zai yadda ya yi duk wani abu da zai daidaita kasar ba.

Shugaban kasar wanda ya yi jawabin ta kafar internet daga fadar asorok da ke Abuja, ya kuma ce, zai yi duk me yiwuwa wajen ganin al’amura sun kyautata a Najeriya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!