Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Buhari zai tafi London ganin likita.

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar gida Najeriya a yau talata don zuwa birnin London na Ingila don ganin likita.

Hakan na cikin wata sanarwa ce mai dauke da sa hannun mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adesina.

Sanarwar ta ce, shugaba Buhari zai gana da shugabannin tsaron kasar nan da safiyar yau talata, kafin daga bisani ya yi balaguron zuwa Ingila.

A cewar mista Adesina shugaba Buhari zai kuma dawo gida Najeriya ne a cikin mako na biyu na watan gobe na Afrilu.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!