Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ba boko haram bane ta kakkabo jirgin mu – Rundunar sojin saman Najeriya

Published

on

Rundunar sojin saman kasar nan ta yi watsi da faifan bidiyo da kungiyar boko haram ta fitar wadda ta ke ikirarin cewa mutanen ta ne suka kakkabo jirgin yakin sojin rundunar da ya yi batan dabo a ranar larabar da ta gabata.

A ranar larabar da ta gabata ne rundunar sojin ta sanar da cewa jirginta na yaki yayi batan dabo yayin wani aiki da ya ke yi a jihar Borno.

A cewar rundunar tana tsammani jirgin ya yi hatsari ne sai dai ba ta da masaniya kan dalilan da ya janyo hatsarin.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar Air Commodore Edward Gabkwet, ta ce, faifan bidiyon da ‘yan boko haram suka fitar na bogi ne kuma bashi da alaka da jirginta da ya yi batan dabo.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!