Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaro: ‘Yan ta’adda za su iya mamaye kasar nan – Gwamna Matawalle

Published

on

Gwamnan jihar Zamfara Mohammed Matawalle, ya yi gargadin cewa ‘yan ta’adda da ke addabar yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya za su iya mamaye kasar nan baki daya, matukar ba a dauki matakin magance matsalar tsaro ba.

Matawalle ya bayyana haka ne a Kaduna, yayin da yake gabatar da wata takarda mai taken “Yaki da yan Bindiga a Arewa maso Yammacin Najeriya” kalubale da samo mafita.

Jawabin nasa wanda ya gabatar a wajen bikin rantsar da sabbin shugabannin kungiyar Arewa Media Writers.

Gwamnan ya koka kan yadda Arewa bata da wani kyakkyawan shugabanci da zai jagorantar da ita domin fita daga halin da ta ke ciki, yana mai cewa  manyan kasar ba su da wani buri da ya wuce samun karfin siyasa.

Matawalle ya samu wakilcin kwamishinansa na yada labarai, Alhaji Ibrahim Magaji Dosara a wajen bikin.

Ya ce, rashin goyon baya daga wani bangare na jiga-jigan ‘yan siyasa masu sha’awar yin amfani da rikice-rikicen don samun matsayi a siyasa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!