Kaduna
Tsaro: Za mu datse layukan sadarwa a Kaduna – El-rufai
Gwamnan Kaduna Nasiru El-Rufai ya bukaci mazauna jihar da su shirya don kuwa za a katse layukan sadarwa.
El-Rufai ya bayyana hakan a hirarsa da manema labarai a ranar Talata.
Gwamnan ya ce rufewar ba za ta shafi jihar baki ɗaya ba, illa ƙananan hukumomin da ke makwabtaka da Zamfara da Katsina inda ake ci gaba da daƙile harin ƴan bindiga.
A cewar El-rufai sojoji da sauran hukumomin tsaro sun shawarci gwamnati da ta rufe layukan sadarwa a wasu ƙananan hukumomi, kuma da zarar sun sanar da ƙananan hukumomin za a ɗauki matakin.
Gwamnatin Kaduna ta musanta jita-jitan da ke cewa zata dakatar da layukan sadarwa a Jihar
“Amma ina son mutanen jihar Kaduna su kwana da shirin ko-ta-kwana na datse layukan sadarwa a jihar” a cewar gwamnan.
Gwamna El-rufai ya kuma ce matakin ya biyo bayan samun rahoton yadda wasu ƴan bindiga da ke jihohin da aka katse layin waya, suka tsallaka wasu ƙananan hukumomin jihar Kaduna don yin waya ga iyalan waɗanda suka sace.
Sai dai ya ce ba zai ambaci ƙananan hukumomin da abin zai shafa ba amma ƙananan hukumomin da a kullum suke fuskantar ayyukan ta’addanci su sun san kansu.
You must be logged in to post a comment Login