Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

Tsohon Dan takarar Gwamna a jahar Gombe Hon. Jafar Abubakar Kwadon ya fice daga Jam’iyya APC

Published

on

Tsohon Dan takarar kujerar Gwamna a jahar Gombe har Karo biyu Honourable Jafar Abubakar Kwadon ya fice daga jam’iyyar APC a ranar Alhamis data gabata

A wata takardar data samu sa hannunsa daya aikewa shugaban jam’iyyar APC na mazabarsa dake Kwadon a karamar hukumar Yamaltu Deba, Jafar yace ya fita daga jam’iyyar ce a bisa radin kansa sakamakon maida shi saniyar ware da aka yi. Ba a tuntubarsa a harkokin jam’iyyar bare kuma na Gwamnatin da suka bada gudumawa aka kafa.

Jafar ya tsaya takarar Gwamnan Gombe har Karo uku a inuwar jam’iyyar ADC a zabukan 2007, 2011 da kuma 2015 da suka gabata, wadda yazo na Uku a zaben 2011.
A shekarar 2018 Jafar ya fice daga jam’iyyar ADC inda ya koma jamiyyar APC a shekarar 2018 da suka hada karfi da Dan takarar ta Alh Muhammad Inuwa Yahaya, suka kuma yi nasara a zaben 2019.
Har ya zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto Jafar dai bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba, yace dai yana Kan tuntubar Magoya baya da Abokan arziki da zasu tsaida jam’iyyar da zai koma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!