Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsohon gwamnan Kaduna ya sauya sheƙa

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Mukhtar Ramalan Yero, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Ramalan Yero ya sanar da ficewar tasa ne a wani bayani da ya yi wa manema labarai yau Litinin a garin Kaduna.

Tsohon gwamnan ya ce ya koma APC ne bisa dalilan ƙashin kansa bayan ya tattauna da makusantansa a harkar siyasa.

Idan za a iya tunawa dai, tun a watan Oktoban bara ne Mukhtar Ramalan Yero, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP.

Mukhtar Ramalan Yero, ya yi gwamnan jihar ta Kaduna a ƙarƙashin jam’iyyar PDP daga shekara ta 2012 zuwa 2015 bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar Patrick Yakowa a hatsarin jirgin helikwafta.

Bayan nan ne kuma ya yi takarar gwamnan jihar a jam’iyyar PDP sai dai bai samu nasara ba, inda daga bisani ya yi ta yin takarar gwamnan jihar, sai dai bai samu nasarar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!