Connect with us

Labarai

Tsohon kyaftin a Kungiyar Manchester City ya nemi a sallami Pep Guardiola

Published

on

Tsohon kyaftin din Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City dake kasar ta Ingila Yaya Toure ya ce ya kamata Kungiyar ta sallami mai horas da ‘Yan wasan ta Pep Guardiola, sabo da gaza daukan gasar cin kofin zakarun turai ta Champion League.

Toure, ya ce lashe kofin zakarun turai na daya daga cikin dalilan da suka sanya a ka kawo shi zuwa kungiyar a shekarar 2016.

Amma kuma yanzu haka ya kwashe shekaru 4 baije koda wasan karshe ba a kofin na Champion league, a don haka ya kamata ya matsa a kawo wanda zai iya.

Goardiola, dai ya lashe kofin na zakarun turai da Kungiyar Barcelona, amma ya kasa daukan kofin a Kungiyar Bayer Munich da Manchester City.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!