Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda take wakana a hada-hadar siyan ‘yan wasa a Nahiyar Turai

Published

on

Daga Abubakar Tijjani Rabiu

 Mai horas da Kungiyar kwallon kafa ta  Tottenham Jose Mourinho ya ce yana son ya dawo da dan wasan Real Madrid da Wales Gareth Bale.

Rashin cimma matsaya ya jinkirta shirin Manchester United na dauko dan wasan Borussia Dortmund dan kasar Ingila, Jadon Sancho.

Haka zalika mai yiwuwa Manchester United ta ba da mai tsaron ragarta dan kasar Argentina Sergio Romero, ga Aston Villa a wani bangare na yarjejeniyar dauko dan wasan Ingila, Jack Grealish.

Chelsea da Atletico Madrid suna son dauko dan wasan Juventus da Italiya Federico Bernardeschi.

Benfica da Valencia suna son dauko dan wasan Manchester United da Brazil Andreas Pereira.

A karo na uku Leeds ta nemi daukodan wasan Brighton dan kasar Ingila Ben White – kuma an yi amanna ta ware kusan £25m don dauko dan wasan.

Wolves ta shirya domin sayar da dan wasan Sufaniya Adama Traore a farashin mai gwaɓi duk da yake saura shekara uku kwantaragin dan wasan ta kare.

Tottenham tana son aron dan wasan Liverpool dan kasar Ingila Rhian Brewster.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!