Labarai
Tsohon shugaban hukumar kwastam ya rasu
Tsohon shugaban hukumar hana fasakwauri ta kasa Kwastam Dikko Inde rasu a yau Alhamis 18 ga watan Fabrairu yana da shekaru 61.
Rahotanni daga jihar Katsina sun tabbatar da mutuwar tsohon shugaban hukumar ta kwastam, a Abuja bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Marigayin, wanda ɗan asalin garin Musawa na jihar Katsina, ya rasu ya bar mata ɗaya da yara uku, maza biyu da mace ɗaya.
An haifi Abdullahi Dikko Inde ranar 11 ga watan Mayun 1960. Ya kuma shiga aikin kwastam a shekarar 1988.
Ya zama shugaban hukumar kwastam a watan Agustan 2009 inda ya sauka a watan Agustan 2015.
You must be logged in to post a comment Login