Kiwon Lafiya
Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya bukaci a kawo karshen yunwa da talauci a Najeriya
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya jaddada kudirin bukatar da ke akwai wajen kawo karshen yunwa da talauci, tare da lalubo hanyoyin da za’a bi wajen inganta bangarorin samar da abinci a fadin kasar nan.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne, lokacin da yake jawabi yayin wani taro da kungiyar kawar da yunwa ta shirya a jihar Sokoto, tare da cewa ayyukan kungiyar da za a fadada shi zuwa sauran jihohin Najeriya zai mayar da hankali ne kan yadda za a inganta harkokin noma, a wani bangare na samar da isasshen abinci ga al’ummar Najeriya.
Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa a yanzu kungiyar za ta fara gudanar da ayyukan ta a wasu jihohi 6 da suka hadar da Sokoto, Kebbi, Borno, Ogun, Ebonyi da kuma Benue, tare da cewa suna aiki ne tare da wasu kungiyoyin bayar da agaji na kasa-da-kasa duk da nufin kawo karshen yunwa da talauci a fadin tarayyar Najeriya.
A nasa jawabin, mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III cewa ya yi matsawar al’umma suna son ciyar da kasar su ko kuma yankin su gaba, akwai bukatar su mayar da hankali sosai ga bangaren noma.
Alhaji Sa’ad Abubakar ya kuma ce abin takaici a yanzu shi ne, yadda mutane suka watsar da noma, sakamakon bayyanar danyen mai, inda ya ce aikin kungiyar zai taimaka gaya wajen cimma manufofin gwamnatin tarayya na inganta harkokin noma a Najeriya.