Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Magance matsalar yunwa da rashin aikin ne kadai hanyar magance matsalar  mayakan Boko Haram-Obasanjo

Published

on

Tsohon shugaban Najeriya chief Olusegun Obasanjo ya ce ta hayar magance matsalar yunwa da rashin aikin yi a kasar za’a iya  magance matsalar  mayakan kungiyar Boko Haram.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a garin Maidugurin jihar Borno lokacin da ya ke jagorantar taron shirin kawar da yunwa wanda ya hadar da gwamnatin tarayya da kuma kungiyoyin kishin al’umma a fadin duniya.

Obasanjo ya ce bincike ya nuna cewar mafiya yawan mayakan boko haram ba wai sun dauki makami ne domin ya ki da kasa ba ko kuma ciyar da wani addini gaba sai dai don su yaki yunwa da kuma rashin aikin yi.

Shi dai Obasanjo shi ne ke jagorantar shirin muradan karni wanda ke kula da yaki da yunwa a Najeriya, inda kuma yake jagorantar gangamin yaki da yunwar a wasu sassan kasar nan

Ya kuma ce manufofin shirin muradan karni guda goma 17 a kasashen duniya, yaki da yunwa shi me na biyu.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!