Kiwon Lafiya
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ziyarci gidajen jarida a jihar Ogun
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ziyarci shalkwatar yan jaridu dake jihar Ogun a yau, inda yayi rajistar zama mamba a gamayyar kungiyar siyasa da aka kaddamar da ita a jiya wadda aka alakanta ta da shi.
Rahotanni sun bayyana cewa tun zamanin da Tsohon shugaban kasa Olusegun ke kan mulki a shekarar 1976 zuwa 1979 zamanin soji da kuma shekarar 1999 zuwa 2007 zamanin farar hula har bayan saukar sa daga mulki bai taba ziyartar wata shalkwatar yan jaridu ba.
Cikin wadanda ke cikin gamayyar kungiyar akwai tsohon gwamnan jihar Cross River Donald Duke da kuma tsohohuwar Ministan tarayya Mrs Dupe Adelaja da kuma tsohon Gwamnan Osun Olagunsoye Oyinlola da sauran mutane da dama.
Obasanjo ya yi rajistar zama mamba a gamayyar kungiyar da misalin karfe 12 da minti 52 na ranar yau, inda ya bayyana cewa samar da gamayyar ya zama wajibi don ciyar da kasar nan gaba da kuma inganta Dimuradiyyar ta.
Ya kuma kara da cewa dole ne Najeriya ta samu cigaba kamar yadda sauran takwarorin ta da suka samu yancin kai tare suka samu, musamman ga matasa da matan kasar nan, inda ya ce su ne su ka fi shan wahala idan wata matsala ta taso a kasar nan.