Manyan Labarai
Tubabbun masu garkuwa sun saki mutane 372 a Zamfara
Tubabbun ‘yan bindiga a jihar zamfara sun mika mutanen da suka yi garkuwa da su mutum 372 tare da bindigogi 240 ga shirin wanzar da zaman lafiya na jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Zamfara Usman Nagogo, wanda shi ne shugaban kwamitin na wanzar da zaman lafiya ne ya bayyana hakan a jiya Lahadi 22 ga watan Satumba yayin taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki na kwamitin a garin Bakura.
Haka kuma ya kara da cewa sun gano ‘yan ta’addar ba wai iya Fulani makiyaya ba ne, kamar yadda ake yada jita-jita, yana mai cewa, ‘yan ta’addar sun fito ne daga kabilun kasar nan daban-daban.
Kwmishinan ‘yan sandan na jihar zamfara ya kuma zargi jami’an tsaron sa kai da ake kira da ‘yan sintiri da kara ta’azzara ayyukan ta’addanci a jihar.
Usman Nagogo ya kuma bayyana gamsuwarsa da irin nasarar da kwamitin ya samar daga kafa aikinsa zuwa yanzu, inda ya cewa a baya an rufe wasu daga cikin kasuwannin jihar sakamakon matsalar tsaro, amma a yanzu an bude kasuwannin kuma Fulani na gudanar da kasuwancin su ba tare da wata matsala ba.
Kwamishinan ‘yan sandan ya kuma bukaci al’ummar jihar das u mara wa kwamitin baya tare da taya su da addu’o’in samun nasara a ayyukan su.
Yayin taron dai an tattara masu ruwa da tsaki a rikice-rikicen jihar da suka hadar da ‘yan sintiri da shugabannin Fulani masu rike da sarautun gargajiya da sauransu.