Labarai
Turkiyya ta ɗebe ma’aikata 9 daga BBC Hausa
Gidan Talabijin da Rediyo na Turkiya ya kwashe wa BBC Hausa ƙwarrarun ma’aikata guda 9.
A wani lamari irinsa na farko cikin gwamman shekaru BBC Hausa za ta yi rashin ƙwararrun ma’aikatanta da suka shafe sama da shekara 10 suna aiki da ita.
Manyan jiga-jigai ne aka ɗebe da suke kula da shafukan BBC na Intanet da kafafen sada zumunta.
Akwai fuskoki da dama da aka sani da suke gudanar da shirye-shirye na intanet a BBC Hausa na yau da gobe.
Gidan Talabijin da Rediyo na Turkiya ya gudanar da wani gagarumin shirin da zai mayar da hankali kacokan kan nahiyar Africa, musamman masu amfani da harshen Hausa.
Gidan Talabijin da Rediyo na Turkiyya ya ɗauki ƙwararren mai kula da shafin BBC Hausa Nasidi Adamu Yahaya a matsayin shugaban sashen Hausa na Turkiyya.
Ya kuma ɗaukar masa ƙwararrun mataimaka biyu da suka hada da Halima Umar Saleh wadda fitacciyar mai gabatar da shirye-shiryen intanet irinsu “Zamantakewa” da kuma Ishaq Khalid ƙwararren mai rahoton BBC cikin harsunan Hausa da Turanci.
Sai kuma ɓoyayyiyar fuskar da ba a fiya ganinta ba, wato babban ƙwararren da ke kula da shafukan BBC Hausa na Facebook, Instagram da Twitter Umar Rayyan wanda zai ci gaba da yin irin aikinsa na BBC a Turkiyyan.
Cikin ma’aikatan da aka ɗauka akwai matashin nan mai gabatar da shirye-shirye a kafafen sada zumunta Abdulbaki Aliyu Jari.
Freedom Radio Nigeria ta gano cewa sauran sun haɗa da gogaggen dan jaridar nan Mustapha Musa Kaita, sai kuma Abdussalam Usman Abdulkadir da Bashir Idris Abubakar waɗanda su kuma masu ɗaukar bidiyo ne a BBC.
Bayan sashen Hausa BBC, TRT ta kuma tsallaka BBC Yoruba inda a nan ma ta ɗauke babban mai kula da shafukansu na intanet Abdulwasi’u Hassan.
Koda ya ke bamu tuntuɓi BBC Hausa ba, amma ga masu bibiyar kafar ta BBC Hausa za su yi amannar tafiyar waɗannan ma’aikata lokaci guda, zai zama gagarumin koma baya ga sashen.
You must be logged in to post a comment Login