Connect with us

Labarai

Tinubu ya gana da shugaban jam’iyyar SDP

Published

on

Shugabannin jam’iyyar SDP da ƙungiyar IPAC sun jaddada bukatar a sake duba dokokin zaɓe domin tabbatar da sahihin zaɓe kafin babban zaɓen shekarar 2027. Sun bayyana hakan ne bayan wata ganawar sirri da suka yi da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja

.

Shugaban SDP na ƙasa, Farfesa Sadiq Umar Gombe, ya ce tattaunawar da suka yi da shugaban ƙasar ta mayar da hankali ne kan yadda za a ƙarfafa dokokin zaɓe domin dawo da amincewar jama’a ga tsarin dimokuraɗiyya. Ya ƙara da cewa ƙarancin masu kaɗa ƙuri’a a zaɓen ƙananan hukumomin babban birnin tarayya Abuja, alama ce da ke nuna cewa mutane na rasa ƙwarin gwiwa ga tsarin zaɓe.

 

 

Shi ma shugaban IPAC na ƙasa, Dakta Yusuf Dantalle, ya bayyana cewa sun tattauna kan wasu batutuwa a dokar zaɓe, musamman tsarin zaɓen fidda gwani na kai tsaye ko na wakilai da kuma tura sakamakon zaɓe ta hanyar fasahar zamani. A nasa bangaren, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na SDP a zaɓen 2023, Adewole Adebayo, ya bukaci ‘yan siyasa da su guji mayar da zaɓen 2027 na “mutuwa ko rai”, yana mai cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne nasarar Najeriya baki ɗaya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!