Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Twitter: Gwamnatin Najeriya ba ta kyauta ba – inji cibiyar CITAD

Published

on

Cibiyar (CITAD) dake bunkasa fasahar sadarwa da ci gaban al’umma, ta yi kira ga majalisun dokokin tarayya da su dauki matakin gaggawa bisa umarnin gwamnatin tarayya na toshe kafar sada zumunta ta twitter.

 

Shugaban cibiyar Malam Yunusa Zakari Ya’u, shine ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai da cibiyar ta gudanar a ranar asabar a Kano.

 

Malam Yunusa Zakari, ya ce, gwamnatin tarayya ba ta kyauta ba da ta dauki matakin toshe twitter, kuma wannan mataki ba zai ragi kamfanin twitter ba illa raba ‘yan Nigeria da ayyukan su.

 

Cibiyar ta kara da cewa, hana yin amfani da wata kafa ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!