Labarai
Twitter: Mun dakatar da kamfanin bisa tsarin dokar kasa – Buhari
Gwamnatin tarayya ta ce dakatarwar da ta yiwa kamfanin Twitter daga aiki a Najeriya ya dace da dokokin kasar nan.
Ministan yada labarai da raya al’adu Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da harkokin yada labarai a Talatar nan.
Alhaji Lai Muhammad ya ambaci sassa daban-daban na kundin tsarin mulkin Najeriya don nuna goyon baya ga matakin da aka dauka a hukumance na dakatar da kamfanin da kuma barazanar da barin sa zai haifar dangane da kalubalen tsaro da ake fuskanta kasar.
A cewar Lai Mohammed a yanzu gwamnatin tarayya ta fara tattaunawa da kamfanin na Twitter domin shawo kan lamarin, sai dai har zuwa yanzu dakatarwar na ci gaba da aiki.
Tuni dai Kamfanin na Twitter ya rubutawa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari wasika yana neman gwamnatinsa da ta janye matakin da ta ɗauka na toshe harkokinsa daga ƙasar nan.
Kamar yadda mai taimakawa ministan yaɗa labarai da raya al’adu, Segun Adeyemi, ya bayyana ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Wannan na zuwa ne a lokaci guda da mambobin majalisar wakilai ke kushe matakin da gwamnati ta ɗauka na toshe twitter daga Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login