Kiwon Lafiya
UBEC: akwai Malamai dayawa da basuda kwarewar aiki
Hukumar kula da ilimin bai daya ta Najeriya UBEC ta ce kaso 57 na malaman makarantu a Najeriya ne suke da kwarewar aiki.
Shugaban Hukumar ta Dr Hamid Bobboyi ne ya bayyana haka a Kaduna lokacin da ya ke gabatar da wata mukala mai taken matsayin ilimi a jihar Kaduna.
Ya ce an samu karuwar malamai daga dubu dari takwas da arba’in da daya da dari bakwai da goma sha shida a shekarar dubu biyu da takwas zuwa miliyan daya da rabi a shekarar dubu biyu da goma sha takwas.u
Sai dai ya ce kaso arba’in da uku na malaman wadanda adadinsu ya kai dubu dari shida da arba’in da arba’in da biyar ba su da kwarewar aiki.