Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

UCL: Chelsea tayi nasarar kaiwa zagaye na Quarter Final

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da ke kasar Ingila, tayi nasarar kaiwa zagaye na dab dana kusa da karshe a gasar cin kofin zakarun turai Champions League. 

Chelsea tayi nasara ne bayan doke Lille da ci 2-1 a ranar Laraba 16 ga Maris din 2021.

Wasan da ya gudana a  filin Stade Pierre na kasar Faransa karkashin jagorancin alkalin wasa Davide Massa dan kasar Italiya.

A minti na 37 ne dan wasa Yılmaz ya fara zura kwallon farko a bugun daga kai sai mai tsaran gida.

Sai dai a minti na 45 dan wasan kasar Amurka  Pulisic ya warware kwallon da aka zura musu.

Kafin daga  bisani kyaftin din kungiyar Azpilicueta ya kara kwallo ta biyu a minti na (70′) da wasan.

Chelsea dai ta bi sahun kungoyi irinsu  Manchester City, Liverpool duka daga kasar Ingila da suka kai tsage na Quarter Final.

Sauran sune  Real Madrid, Atletico Madrid da Villarreal daga kasar Spain, sai  Bayern Munich daga Jamus da kuma Benfica daga kasar Portugal.

Jadawalin na wasannin kusa da karshe zai gudana a ranar Juma’a 18 ga Maris  mai zuwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!