Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

UCL :Real Madrid ta kai wasan karshe bayan doke Manchester City

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta kai wasan karshe a kofin zakarun turai bayan doke
Manchester City da ci 3 da 1

Filin wasa na Santiago Bernabeu ne ya karbi bakuncin wasan da ya gudana a ranar Laraba 04 ga Mayun 2022 wanda jumulla gida da waje Madrid ta doke City da ci 6 da 5.

Dan wasa Riyard Mahrez ne dai ya fara zura kwallon farko a minti na 73, bayan tinda fari a wasa zagaye na farko da suka fafata Manchester City ta lallasa Madrid da ci 4-3.

Sai dai bayan sauyin mai horar da Real Madrid Carlo Ancelloti yayi, na shigo da Rodrygo ya sa dan wasan zura kwallaye biyu a mintina na 90 da 91.

Bayan karin lokaci 30 wato Extra Time dan wasa Karim Benzema ya zura kwallo ta uku a bugun daga kai sai mai tsaran gida a minti na 95.

Yanzu haka dai Real Madrid zata buga wasan karshe da Liverpool a ranar 28 ga Mayun da muke ciki a birnin Fari na kasar Faransa.

Real Madrid dai itace kungiya daya dilo da ta fi ko wacce lashewa da jumulla 13 inda ta ke yunkurin lashe na 14 a tarihi.

Manchester City kuwa sau daya ta taba zuwa wasan karshe a kakar wasannin 2022/2021 inda tayi rashin nasara a hannun Chelsea a wasan karshe da ci 1-0.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!