Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

UEFA: Ta dakatar da mai tsaron ragar Ajax zuwa shekara daya

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai UEFA ta dakatar da mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Ajax Andre Onana daga buga wasanni tsawon shekara daya bisa zarginsa da amfani da kwayoyin kara kuzari.

Kungiyar ta Ajax ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar inda ta ce Onana ya yi amfani da maganin da matarsa ke sha ne bisa kuskure lamarin da ya sanya aka samu alamar kwayoyin yayin gudanar da gwaji ga ‘yan wasa.

Ajax dai na fatan hukumar zata sassauta dakatarwar da tayi wa dan wasan na tsawon shekara daya duba da yadda lamarin ya faru bisa kuskure kuma kwayoyin bana karin kuzari ba ne.

Haka zalika kungiyar zata daukaka kara zuwa kotun hukunta laifukan wasanni wato CAS don kare mutuncin dan wasan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!