Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

NFF: Alloy Agu ya fara karbar albashin da yake bi

Published

on

Mai horas da masu tsaron ragar Super Eagles Alloy Agu ya tabbatar da cewa hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta fara biyanshi wasu daga cikin kudaden albashi na watannin 22 da yake bin hukumar.

Shugaban hukumar ne Amaju Pinnick ya yi alkawarin fara biyan wani kaso daga cikin kudaden da Alloy Agu da kuma Gernot Rohr suke bi a wannan lokacin.

NFF ta fara biyan albashin ma’aikatan dake bin ta bashi

Haka zalika a ranar Asabar da ta gabata Pinnick ya ce hukumar ta tura wa ma’aikatan wasu kudaden domin rage yawan bashin.

Pinnick ya kuma ce, “Babu wanda zai so a biyoshi bashi. Yanzu akwai karacin samun kudaden shiga a hukumar duba da yadda masu daukar nauyin hukumar basa iya biyan kudaden akan lokaci sakamakon matsin tattalin arziki sanadiyyar cutar Corona.”

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!