Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Umara: Gurare biyu maniyyatan bana za su ziyarta a ƙasa mai tsarki – NAHCON

Published

on

Hukumar kula da aikin hajji ta ƙasa NAHCON ta ce, maniyyata aikin Umara a bana za su ziyarci gurare biyu ne kacal a ƙasar Saudiyya.

Hukumar ta ce, ga baƙi da suka samu damar shiga ƙasar don yin Umara, ya zama wajibi su yi biyayya ga dokokin da hukumomin ƙasar suka sanya na dakile yaduwar cutar corona.

Hajiya Fatima Usara, wadda ita ce mai magana da yawun hukumar ta bayyana hakan yayin zantawar ta da manema labarai.

Ta ce, guraren da ƙasar ta amince baƙi maniyyata aikin su ziyarta a bana, sune Rauda da kuma birnin Madina, kuma kowanne maniyyaci ba zai shiga ƙasar ba sai ya karbi rigakafin cutar corona.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!