Labarai
UNICEF:Kimanin dalibai miliyan 8 ne basa zuwa makaranta a jihohin Najeriya 10
Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya yace jihohi 10 ciki har da babban birnin tarayya Abuja na da kananan yara miliyan 8 da basa zuwa makaranta.
Jihohin sun hadar da Bauchi da Niger, Katsina da Kano, Sokoto Zamfara Kebbi Gombe Adamawa da kuma jihar Taraba.
A wata sanarwa da asusun ya fitar a jiya Lahadi a yayin bikin ranar yaran nahiyar Africa wakilin asusun a nan Najeriya Peter Hawkings ya ce akwai bukatar a samar da ingantatccen ilimi ga kananan yara musamman mata.
Taken bikin kananan yara na nahiyar Afrika na bana shine yara na da damar samun ingataccen ilimi ko da kuwa a lokacin yaki ne.
Mr. Hawkings ya ce kimanin kananan yara miliyan 10 da rabi ne basa samun damar zuwa makaranta sakamakon ayyukan ta’addanci a yankun jihohin arewa maso gabashin kasar nan.
Ya ce rashin zaman lafiya ya yi sanadiyyar rufe makarantu, haka kuma ya hana malaman zuwa makaranta tare da sanya tsoro a zukatan iyaye wajen tura yaransu zuwa makaranta musamman yaran su mata wadanda sune suke cikin daliban da ‘yan ta’adda ke sacewa a makarantun su.
Mr.Hawkings ya ce akwai bukatar mahukunta a wadanan jihohi su daukin matakin gaggawa kan magance matsalar rashin zaman lafiya don tabbatar da cewa kananan yara sun samu ingantaccen ilimi tun daga matakin farko.