Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

AC Milan : Dan wasa Zlatan Ibrahimovic ya kamu da cutar Corona

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta AC Milan da ke kasar Italiya ta bayyana cewa dan wasanta Zlatan Ibrahimovic ya kamu da kwayar cutar Corona.
Ibrahimovic mai shekaru 38, wanda kuma tsohon dan kasar Sweden ne, ya killace kansa gidansa, kamar yadda kungiyar ta sanar.
Sakamakon gwajin kwayar da aka yi ma san a biyu ne ya tabbatar da cewa yana dauke da cutar.

Ko jiya laraba mai tsaron bayan AC Milan Leo Duarte shi ma ya kamu da kwayar cutar ta Covid-19.

‘Yan wasan biyu dai ba za su samu damar bugawa AC Milan wasan zagaye na uku na neman cancantar shiga gasar Europa a daren yau da Bodo Glimt ta kasar Norway ba.

A ranar litinin din da ta gabata ne Zlatan Ibrahimovic ya zura kwallayen biyun da suka baiwa Milan damar doke Bolgna a gasar Seire A ta kasar Italiya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!