Labarai
Wada Sagagi ya nemi Shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa yayi murabus
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kano Alhaji Shehu Wada Sagagi ya nemi shugaban jam’iyyar na ƙasa Iyorchia Ayu da ya gaggauta ajiye muƙaminsa.
Sagagi ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai da yammacin Talata, a Shalkwatar jam’iyyar ta jihar Kano.
Ya ce Ayo yayi alƙawarin cewa zai yi murabus idan aka tsayar da ɗan arewa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa domin bai wa yankin Kudu dama.
“To yanzu an tsayar da ɗan Arewa ya kamata ya mutunta wannan yarjejeniya, saboda su ma jama’ar kudu su samu nutsuwar zaɓar mu”.
Ya ƙara da cewa “Ɗan takarar shugaban ƙasa daga Arewa, shugaban jam’iyya daga Arewa, shugaban kwamitin amintattun jam’iyya shi ma daga Arewa, Shugaban gwamnonin jam’iyya shima daga Arewa, ci gaba da tafiya a hakan ba adalci ba ne ga ƴan kudu”.
Alhaji Shehu Wada Sagagi ya ce, shugabannin jam’iyyar PDP na Kano sun jaddada mubaya’a da biyayyarsu ga jam’iyyar PDP.
Sannan ba sau da alaƙa da kowace jam’iyya idan ba PDP ba.
Ya ƙara da cewa, sun yi shirin tallata ɗan takarar jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar da sauran waɗanda jam’iyyar ta tsayar.
Dangane da ɓarakar da jam’iyyar ke fama da ita ya ce, suna ci gaba da tattaunawa domin neman haɗin kan sauran ƴaƴan jam’iyyar.
You must be logged in to post a comment Login