Rahotonni
Waiwaye: Yau shekaru 8 da kai harin Boko Haram na farko a Kano
A ranar ashirin ga watan Janairun shekarar dubu biyu da goma sha biyu ne wasu ‘yan ta’adda suka kai wasu tagwayen hare-haren Boma-Bamai a wasu wurare a nan jihar Kano.
Wuraren da hare-haren suka shafa sun hadar da hukumar kula da shige da fice ta kasa dake kusa da kasuwar sai da wayoyi ta Farm Center da shalkwatar ‘yan sanda shiyya ta daya wato Zone One da Bompai da kuma ofishin hukumar tsaro ta DSS da dai sauran su.
Hakan dai yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama ciki har da jami’an tsaro da kuma manema labarai.
A yau ne dai ashirin ga watan Janairun shekarar 2020 ake cika shekaru takwas da faruwar hare-haren Bama-Baman a Jihar Kano.
Hare-haren da aka samu a shekarar ta dubu biyu da goma sha biyu shine karo na farko da jihar Kano ta fuskanci makamancin sa a tarihin ta, wanda yayi sanadiyyar rasa rayukan jama’a da dama da kuma asarar dukiyoyi masu tarin yawa.
A dai ranar ce al’ummar jihar Kano suka taba karo da makamancin wannan tashin hankali da ya razana kowa tare da kidima jama’a, inda ranar kuma ta shiga cikin ranakun tarihi a jihar Kano kasancewar ba za’a taba mantawa da irin bala’in da al’umma suka tsinci kansu a cikin ba.
Freedom Radiyo ta zanta da wasu mutane da abin ya faru akan idan su a wanccan lokacin game da yadda suke ji idan suka tuna da wannan rana, sai suka ce sunajin babu dadi duba da yadda suka rasa ‘yan uwansu a wancan lokacin.
Shi kuwa shugaban kasuwar sai da wayoyi ta Farm Center Alhaji Tijjani Musa Muhammad cewa yayi tun daga wancan lokacin kasuwar ta himmatu wajen kara inganta tsaro a wani bangare na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma, da kuma tallafawa ‘ya’yan mutanen da suka rasa ransu sanadiyyar harin.
Shima a nasa bangaen mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya yi kira ga al’umma da su dinga sanar da jami’an tsaro idan sunga wani bakon al’amari da basu yadda da shi ba.