Labarai
Wajibi ne a ayyana dokar ta baci a fannin tsaro a Najeriya – Atiku Abubakar

Tsohon ɗan takarar shugabancin kasar nan Atiku Abubakar ya ce har yanzu lokaci bai ƙure ba na ayyana dokar ta ɓaci kan matsalolin tsaro da suka dabaibaye ƙasar nan.
Atiku ya bayyana haka ne a martanin da ya yi kan harin da aka kai a wata makarantar kiristoci a jihar Neja, inda aka yi garkuwa da wasu ɗalibai.
A rubutun da ya yi a kafofin sadarwa, Atiku ya ce, “wannan abin takaici ne.
Mutane nawa za a ƙara rasawa kafin a ɗauki matakin mai ƙarfi da ya dace? ina ganin har yanzu lokaci bai ƙure ba kan ayyana dokar ta ɓaci kan matsalar tsaro domin magance matsalar.”
You must be logged in to post a comment Login