Kasuwanci
Wajibi ne mutane su karbi sauyin sabon kudi: Alhaji Ado Muhammad
- Al’umma su karbi sauyin da babban bankin kasa CBN yazo da shi a kan hada-hadar kudi.
Masani kan harkokin hada-hadar kudi kuma kwararren akanta a Kano Alhaji Ado Muhammad, ya ce, wajibi ne al’umma su karbi sauyin da babban bankin kasa CBN yazo da shi a kan hada-hadar kudi.
Alhaji Ado Muhammad ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio da safiyar yau, wadda tattaunawar ta mayar da hankali kan batun daina amfani da tsaffin kudin da aka sabunta a karshen watan da muke ciki.
Alhaji Ado Muhammad ya kuma bukaci jama’a da su guji biyewa masu yada jita-jitar cewa, za a kara wa’adin amfani da tsoffin kudin.
Don haka yake kira ga al’umma da suyi kokari wajen ganin sun canza kudinsu akan lokaci don gujewa asara.
Rahoto: Nura Bello
You must be logged in to post a comment Login