Labarai
Wajibi Nyesom Wike ya nemi afuwar shugaba Tinubu bisa cin mutumcin jami’in sojan Najeriya da ake zargin sa: Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai mai ritaya

Tsohon Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai mai ritaya, ya bayyana cewa wajibi ne Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya nemi afuwa daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma rundunar sojin Najeriya bisa abin da ya aikata wa wani jami’in soja.
Buratai ya ce abin da ya faru tsakanin Wike da sojojin ya nuna rashin girmama rundunar tsaro da kuma rashin bin tsarin doka, yana mai jaddada cewa bai dace jami’in gwamnati ya nuna wa jami’in soja irin wannan dabi’ar ba, musamman a bainar jama’a.
Ya ce Wike ya kamata ya bai wa Shugaban kasa, wanda shi ne Kwamandan Rundunonin Tsaro, da kuma sojojin kasar nan, hakuri bisa wannan lamari.
You must be logged in to post a comment Login