Labarai
Wanda ke dauke da cutar HIV zai iya Auren wanda bashi da Ita – SAKA
Masana a fannin lafiya sun ce Mai dauke da cutar Mai karya garkuwar jiki wato HIV zai iya auren Wanda bashi da cutar, har su haifi yaran da basa dauke da cutar.
Dakta Usman Bashir shugaban hukumar da ke kula da cuta mai karya garkuwar jiki ta nan Kano SAKA ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio.
Dakta Usman Bashir ya ce ana samun nasarar yin auren ne bayan bin wasu dokokin da za’a gindayawa ma’auratan kafin aure.
Ya Kuma Kara da cewa wannan ce ta sanya ya zuwa yanzu an fara samun karancin Yara masu dauke da cutar, biyo bayan wannan sabon tsarin da aka fitar dashi.
Shugaban hukumar SAKA Dakta Usman ya ce a kimanin mutane miliyan biyu ne ke dauke da cutar a kasar nan , yayin da Kano ke da kimanin mutane dubu 32,800.
You must be logged in to post a comment Login