Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Wani  dan Boko haram ya mika kansa ga Rundunar sojin Najeriya

Published

on

Rundunar Sojin kasar nan ta tabbatar da cewa wani  dan Boko Haram mai suna Sajeh Yaga, ya mika kansa ga dakarun Operation Hadin Kai a jihar Borno.

Shafin X na kwararren  mai sharhi kan yaki da tada kayar baya a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya tabbatar da  cewa, dan ta’addan ya mika wuya ne tare da bindiga kirar Ak47 guda daya, Mujallun Bindigar  guda hudu da wayar hannu ta Tecno guda uku da sauran wasu  kayayyakin.

Dan ta’addan, wanda ya tsere daga sansanin Boko Haram da ke Yale, a dajin Sambisa, ya mika kansa ga dakarun bataliya ta 112 a Mafa a jiya Lahadi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!