Connect with us

Addini

Wani maniyyacin Najeriya ya rasu a kasar Saudiyya

Published

on

Wani maniyyacin daga cikin alhazan jihar Abiya ya rasu a birnin Makka.

Marigayin mai suna Alhaji Sale, wanda shi ne shugaban kasuwar shanu ta Lokpanta da ke jihar Abiya, ya rasu ne a daren jiya Litinin.

Wakilin hukumar aikin hajji ta Najeriya NAHCON, Alhaji Ibrahim Orjibulam, ne ya tabbatar da rasuwar mamacin.

Sanarwa ta ce, ana sa ran yi wa marigayi Alhaji Sale, jana’iza yau Talata a masallacin Harami da ke Birnin Makka.

Rahotonni sun bayyana cewa, wannan ne karo na biyu da aka samu rasuwar alhazan Najeriya bayan rasuwar wata mata ‘yar asalin jihar Edo.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!