Connect with us

Labaran Kano

Wani matashi yayi garkuwa da wani yaro a Kano

Published

on

Anyi nasarar damke matashin ne a lokacin da ake zargin shi da yin garkuwa da wani yaro dan shekaru goma, bayan da iyayen yaron suka yi kararshi.

Matashin wanda dan uwan matar ne ya nemi masauki a gidan, inda matashin yayi amfani da wannan dama ta hanyar yin garkuwa da dansu mai shekara goma.

Matashin ya bukaci Naira dubu dari uku a matsayin kudin fansa, bayan iyayen yaron sun biya wannan kudi sai ya kasha shi ya kuma jefar da gawarsa a kauyen Minjibir.

Rundunar ‘yan sanda ta Kano ta yi holin masu yin garkuwa da mutane

Masu dauke da cuta mai karya garkuwa na fuskantar tsangwama- Nuhu Tela

Masu garkuwa da mutane sun sace dan jaridar Borno

Iyayen yaron sun bayyana cewa  sun ji labarin an tsinci gawar dansu a kauyen Minjibir, inda suka tarar har mutanen da suka tsinci gawar yaron sun yi jana’izar sa kamar yadda addinin Islama ya tanada.

‘jami’an ‘yan sanda dai sunyi nasarar kamo wannan matashi a jihar Kaduna, tare da gurfnar dashi a gaban  kotu domin girbar abin da ya shuka.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,462 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!