Connect with us

Labarai

Dubun wata budurwa ya cika bayan da aka yi zargin ta da sace gwala-gwalai

Published

on

Ita dai wannan budurwar mahaifiyar ta ce ta kai karar ta ofishin kare hakkin dan Adam, inda ta bayyana cewa yarta tana satar mata kudade da gwalagwalai tana kaiwa saurayinta , kuma hakan na zuwa ne daidai lokacin da ta nemi gwalagwalan nata ta rasa.

A zantawar ta da wakilin mu Aminu Abdu Baka noma, budurwar ta bayyana cewa saurayin nata yana mata barazana ne shine dalilin na na kai masa kudaden.

An dai samu nasarar kama dillalan da suke siyar mata da gwalagwalan yayin da shi kuma saurayin ya gudu.

Kano9: Ina rokon mahukunta su magance satar yara -Sheikh Kariballah Kabara

Ana zargi alkali da baiwa ‘yan sanda satar amsa

Karim Yahaya Lawan Kabara shine shugaban kungiyar kare hakkin bil’adama dake unguwar Sharada, yace akalla budurwa kullun sai ta turawa saurayin dubu goma ko ashirin sannan ta hada masa da gwalagwalan.

Rahotanni na nuni da cewa, budurwar na kaiwa wakilan saurayin da suke karbar kayan, inda ya ce da zarar sun gama bincike za su mika masu laifin wajen ‘yan sanda sannan za su tabbatar da an mika su kotu.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,958 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!