Connect with us

Labarai

Rundunar ‘yan sanda ta Kano ta yi holin masu yin garkuwa da mutane

Published

on

Rundunar ‘yansandan ta jihar Kano tayi holin wasu mutane da take zargi da laifukan  yin garkuwa da mutane da yin fashi da makami, da kuma satar ababan hawa da kuma safarar miyagun kwayoyi a jihar Kano.

Sabon Komishinan ‘yansandan na jihar Kano CP Habu Ahmad Sani, ya sanar da hakan yayin da yake holen kayayyakin laifukan da kuma mutane da ake zargi a yau Laraba a shelkwatar rundunar ‘yan sanda dake nan

Kazlika kwamishinan ‘yan sandan Habu Ahamad Sani, ya ce  rundunar zata cigaba da kama masu laifi a duk inda suke don  ganin zaman lafiya ya wanzu a jihar Kano da ma kasa baki daya.

Kano: Lauyoyi sun yi barazanar gurfanar da kwamishinan ‘yan sanda

Jihar Kano ta sami sabon kwamishinan ‘yan sanda

Rundunar ‘yan sandar jihar Kano ta sake ceto wani yaro a Anambra

Wasu  daga cikin wadanda ake zargin sun yin a dama yayin da kuma wasu daga ciki ke bayyana irin dalilan da ya sanya jami’an ‘yan sandan suka kama su.

Har ila yau wasu daga cikin wadanda ake zargin sun ce sun taka sahun barawo ne amma kuma sun na damar aikata hakan.

A hannu guda kuma wasu ana zargin su ne da siyan kayayyakin sata.

Wakilin mu Abba Isah ya ruwaito cewa komishinan ‘yansandan Kano Habu Ahmad Sani, ya yi kira ga alummar jihar Kano da dinga tallafawa jami’an tsaro ganin lamarin tsaro na bukatar masu ruwa da tsaki kuma na kowa da kowa ne, a don haka na bukatar gudunmawar kowa da kowa.

 

 

Labarai

 Zulum sarkin aiki – Inji masu iya magana

Published

on

Daga Nasiru Salisu Zango

farfesa Babagana Umara Zulum shine Gwamna da yanzu ya zama zakaran gwajin dafi a cikin gwamnonin Nigeria.
Kokarinsa da jajircewarsa wajen kare hakkin talaka a salon mulki irin na salihan baya, shine ya zame masa Jari wajen samun karuwa, ba a jihar Borno Kadai ba har ma a Nigeria baki daya.

Gidan radiyon freedom muryar jama’a zai cigaba da kawo muku Shiri na Musamman akan ayyukan Professor Babagana Umara Zulum gwamnan jihar Borno.

za’a yi ne a tasoshin mu dake Kano da Kaduna.

Shirin zaizo da karfe 7.30 na dare a tashar freedom Kaduna, karfe 8 zuwa 10-10:30 na daren Lahadin a tashar Freedom dake Kano.

HON. Tanimu Tahir Mbaya mataimakin gwamnan jihar Borno a Fannin Yada labarai shine ya dauki nauyin kawo shirin.

A kasance damu Dan Jin kokarin Murucin Kan Dutse Bai fito ba sai da ya shirya.

Rubutu daga Nasiru Salisu Zango

Continue Reading

Labarai

NAHCON ta karrama tashar Freedom Radiyo

Published

on

Hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON ta karrama wakilin Freedom Radio a jihar Kaduna Abubakar Jidda Usman matsayin Dan Jarida mafi kwazo wajen kawo rahoton aikin hajjin da ya gabata.

A yayin wani bikin karramawa da kungiyar masu aike da rahotanni na aikin hajji masu zaman kan su suka shirya a birnin tarayya Abuja an baiwa hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano lambar yabo kan hukumar da tayi fice wajen kula da kayan alhazai.

Kazalika an karrama hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kaduna matsayin wadda tayi fice wajen shirya aikin hajji.

Haka kuma an bada lambar yabo ga hukumar jin dadin alhazai ta birnin tarayya Abuja matsayin wadda tayi fice wajen samar da kyakykyawan masauki.
Sauran jihohin da suka samu lambobin yabo sun hada da Yobe, Kwara da kuma jihar Niger.

Continue Reading

Labarai

Zamu yi aiki tare da hukumar kiyaye hadura ta kasa dake Kano- Haroun Ibini Sina

Published

on

Hukumar Hisbah ta  jihar Kano ta kai ziyara ga hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa a jiya Laraba

Babban kwamandan hukumar Hisbah Sheikh Muhammad Haroun Ibini Sina ne ya jagoranci tawagar hukumar Hisba don kai ziyarar.

Kazalika hukumnar ta Hisba ta nemi hadin kai domin yin aiki tare da jami’an hukumar kiyaye afkuwar haduran don ciyar da al’ummar jihar Kano gaba.

Da yake jawabi shugaban hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa shiyyar Kano Zubairu Mato wanda ya karbi tawagar ta hukumar Hisbar ya nuna farin cikin matuka da wannan ziyara aiki.

Har ila yau Zubairu Mato yayi alkawarin cewa hukumar su zata yi aiki kafada-da-kafada da hukumar Hisbah musamman wajen lura da sanya idanu ga masu amfani da ababan hawa domin tabbatar da zaman lafiya ga al’umma baki daya.

 

 

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!